<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Yunana LW587</title>
<lyrics>[V1]
 YUNANA
 1) Ubangiji ya yi magana da Yunana
 Ya ce &quot;Yunana ka tashi ka je Nineva
 Ka shaida masu bishara domin su tuba
 Gama muguntarsu ta hau zuwa gareni.&quot;

[V2]
 KORUS
 Mu masu bi yau, mu yi biyayya
 Ga magana Ubangiji
 Ubangiji fa ba mutum ba ne
 Don haka mu yi biyayya da maganarsa.

[V3]
 2)Amma Yunana ya tashi domin ya gudu
 Daga fuskar Ubangiji zuwa can Tarshish
 Ya gangara zuwa Yafa ya shiga jirgi
 Yana murna wai ya gudu a fuskar Allah.
 Korus

[V4]
 3)Yunana ya manta Allah yana ganinsa
 Sai Allah ya nuna Ikonsa ga Yunana
 Ya aiko babban iska da haɗari
 Sai Yunana ya tuna Allah yana ganinsa.
 Korus

[V5]
 4)Allah ya shirya babban kifi cikin teku
 Kifi ya haɗiye Yunana har kwana uku
 Nan da nan Yunana ya tuna akwai Allah
 Wane ne zai gudu daga fuskar Ubangiji.
 Korus

[V6]
 5)Cikin duniya yau akwai irin Yunana
 Waɗanda ba su so su bi Ubangiji ba
 Suna ruɗin kansu cewa za su guje shi
 Suna manta Allah ne mahalicin duniya.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>587</hymn_number>
</song>